Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da kuduri da ta haramta auren jinsi daya da kuma nuna kauna da soyayya tsakanin ‘yan luwadi a bainar jama’a.
Sai majalisar wakilai ta amin ce da wan nan kuduri, kuma shugaba Goodluck Jonathan ya rattaba hanu akai san nan ta zame doka.
A baya bayan nan PM Ingila David Cameron yayi barazanar daina bada agaji daga kasashe dake keta ‘yancin ‘yan luwadi da madugo.
Duk da haka luwadi al’amari ne da ake kyamarsa a fadin najeriya mai al’uma milyan 150, kasa mafiya jama’a a duk fadin Afirka.
Dokar wacce majalisar dattijan ta amince da ita talatan nan zata daure duk wadanda aka samu da laifin auren jinsi daya da daurin shekara 14 gidan fursina. Duk wadda ya taimakawa ‘yan jinsi daya suka yi aure ko suka tallata hanyoyin rayuwarsu shima koi ta ma zata sha dauri na shekara 10.
Lokacin da ake muhawara kan dokar, shugaban majalisar dattijai David Mark yace dokar ta nuna tarbiya da al’adun ‘yan Najeriya, kuma kada wata kasa ta nemi yi wa Najeriya shish-shigi cikin dokokin ta.