Wasu ‘Yan Bindiga Sun Halaka Sojojin Nijar A Jibiya

Sojojin Kasar Nijar.

Wasu jami’an tsaron Nijar biyu sun hadu da ajalinsu a wani dajin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina lokacin da suke kokarin damke wasu ‘yan bindigar da suka sace shanu a kauyen Amore na karamar hukumar Dan Issa ta jihar Maradi.

Bayanan da muka tattaro daga yankin Maradi na cewa wannan lamari ya faru ne a cikin daren Litinin wayewar ranar Talata lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kora shanu daga kasuwar kauyen Amore na gundumar Dan Issa suka nufi Najeriya da su ta bangaren Jibiya.

Cikin yanayin ba-zata, motar jami’an tsaron na ‘yan Nijar ta makale a wani wuri mai tabo wanda kuma a daidai nan ne ‘yan bindigar suka masu kwanton bauna lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro biyu.

Magatakardan ofishin shugaban gundumar Madarounfa Abdou Harouna ya tabbatar mana da faruwar wannan al’amari da yayi sanadin mutuwar dakarun Nijar su biyu, koda yake bai yarda in dauki muryarsa ba.

Najeriya da Nijar sun hada gwiwa domin fatattakar ‘yan bindiga ta hanyar wata yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma bayan tabarbarewar sha’anin tsaro a jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto, abinda ya sa askarawan Nijar ke ketara iyaka zuwa Najeriiya a duk lokacin da suka furtumi ‘yan bindigar dake kai farmaki a sassan jihar Maradi.

Rahotanni daga yammacin jiya Talata sun ce waniayarin motoci sama da 10 shake da askarawan Nijar dauke da manyan makamai ya tashi daga Maradizuwa iyakar Najeriya cikin shirin farautar ‘yan bindigar da ake hasashen sun buya a rukukin dajin garin Jibia.

Da ma dai a yayin rangadin daya gudanar a farkon watan nan na Augsta a jihar Maradi shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya yi alkawarin kara yawan jami’an tsaro tare da basu wadatatun kayan aiki domin kawokarshen aika aikar ‘yan bindigar dake ketarowa daga Najeriya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Halaka Sojojin Nijar A Jibiya