A rubuce- rubucen da su ka yi da faransanci wadanda su ka aikata na cewa Buhari bai cancanci a yi masa irin wannan karamawa ba, suna masu kiransa da suna mai aikata laifi wato Criminel.
A ranar 24 ga watan Nuwamba da ya gabata ne shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari daura da taron kungiyar tarayyar Afrika, suka jagoranci bukin bude wani titi mai tsawon kilomita 3.6 da nufin karfafa dadaddiyar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Sai dai tun a wancan lokaci ‘yan Nijer ke nuna ra’ayoyi mabambanta yayin da wasu ke yabawa, wasu kuwa na kushe lamarin saboda a cewarsu tamkar kura ce a ka ramawa aniyarta a bisa la’akari da cewa a shekarar 2020 shugaba Buhari ya radawa wani titin Abuja sunan shugaban Nijer na wancan lokaci Issouhou Mahamadou.
Wasu ma na ganin shugaba Muhammadu Buhari bai cancanci a nadawa wani titi sunansa ba idan aka yi la’akari da halin da Najeriya ta tsinci kanta ciki a tsawon shekarun mulkinsa.
Kawo yanzu hukumomin Nijer ba su yi bayani ba game da wadanan rubuce rubuce na batanci dake nuna hamayya da radawa titin Nijar sunan shugaba Buhari