A ziyarar aiki da ya kai kasar Italiya don ganawa da shugabannin kasar, shugaba Mohamed Bazoum ya bukaci a kulla yarjejeniya ta daukar ma’aikata daga kasashen Afirka zuwa Turai domin samin bakin zare ga matsalar bakin haure.
Bazoum ya yi magana ne yayin ganawa da shugaban Italiya Sergio Mattarella, tare da shugabannin kasashen Afirka a wani taro a birnin Rome.
Bazoum ya fada a wata hira da wata jaridar kasar Italiya a ranar Juma'a cewa yakamata kasashen Afirka da na Turai su amince da kayyade adadin bakin haure na Afirka, wanda ya dace da bukatun aikin yi a kasasen Turai.
Haka kuma ya yi kira da a cimma yarjejeniya kan adadin ‘yan Afirka da kowace kasa ta Turai ke bukata a kasuwar ’yan kwadagonta don taimakawa wajen magance matsalar bakin haure da safarar mutane.
Daruruwan ‘yan Afirka ne ke kokarin tsallakawa Turai ta barauniyar hanya mai hatsarin gaske, a kokarinsu na neman rayuwa mai inganci lamarin dake haifar da asarar rayuka.
Domin jin cikakken bayani saurari rahotan Mahmud Hamid cikin sauti.