BONN, GERMANY - Wannan kira na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnatocin kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea suka fitar a matsayin martani ga shirin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO kan mayar da Bazoum akan kujerar mulki.
Gwamnatocin soji a kasashen uku sun lashi takobin marawa sojojin da suka yi juyin-mulki a Nijar baya, bayan wasu sharuda da takunkumai da ECOWAS ta kakabawa sojojin na Nijar.
Kusan ana iya cewa rikicin juyin-mulkin Nijar na sake daukan sabon salo, musamman tun lokacin da ECOWAS ta fitar da wata sanarwa da ke aike gargadi mai karfi da wasu sharuda masu tsauri kan sojojin da suka hambarar da Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki.
Sai dai a daidai lokacin da aka zuba ido da kidaya wannan wa’adi domin ganin yadda abubuwa za su karkare, sai gashi a wannan Talatar an wayi gari da martini daga kasashen Afirka uku na Mali, Guinea da Burkina Faso, da duk sojoji suka yiwa gwamnatin farar-hula juyin-mulki.
Wannan sabon takun-saka ya jefa ‘yan Nijar mazauna Turai cikin fargaba abin da ya kai ga Mohammed Momo wani mazaunin Jamus ke ganin cewa ai ECOWAS ba ta damu da damuwar ‘yan Nijar ba ko kadan.
Duk da cewa ECOWAS gamayya ce ta kasashe 15, kusan kasashe biyar dake cikinta yanzu haka sojoji ne ke mulki, wannan dalili ne da ya sa Malama Hadiza ita mazauniya a Jamus ke ganin irin wannan barazana na tattare da illoli
Sai dai ga wasu masu sharhi kan siyasar Afrika kamar Sadik Abba da ke zaune a birnin Paris na kasar Faransa, tura ce ta kai bango kuma tun da an kai ga hambararr da gwamnatin Bazoum, to abin da ya dace ayi yanzu sai dai ayi hakura a rungumi kaddara.
Yanzu dai ana ci gaba da tafka mahawara a ciki da wajen kasar Nijar kan ko matakin da kungiyar ECOWAS ke shirin dauka na tura sojojin kungiyar Nijar don kawo karshen juyin mulkin zai yi tasiri, ko kuma za a ga wani sauyi bayan barazanar sojojin kasashen Afirka da ke cikin irin yanayi da Nijar ta tsinci kanta.
Saurari cikakken rahoto daga Ramatu Garba Baba:
Your browser doesn’t support HTML5