A dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke cigaba da fama da matsalar karancin mai yanzu haka kasuwar ‘yan bunburuntu ne ta budu inda suke cin karensu babu babbaka. Kuma wadanda suka fi cin wannan kasuwar bayan faggen watau ‘’ Yan –black Markets’’ sune matasa masu jinni a jika, kai wasu lokutan har na yara masu kananan shekaru.
Koda yake wadannan matasa sun ki a dau hotonsu,to amma da jibin goshi sun bayyana yadda suke jin dadi da wannan matsalar man da yanzu ke neman gagaran kundila a jihohin Najeriya.
To sai dai kuma yayin da matasa ke murna, su kuwa masu ababen hawa kokawa suke, sakamakon matsalar da ake ciki.
A kullum dai akan zargi dillalan man, da cewa suke jangwalo wannan matsalar don samun kazamin riba, batun da shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu na IPMAN, mai kula da shiyar Yola, da ta kunshi jihohin Adamawa da Taraba, Alh. Abubakar Salihu Butu ya musanta.
Ya zuwa yanzu dai tuni wasu masu ababen hawa suka koma taka sayyada sakamakon wannan matsalar na tsadar man a Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5