Furodusan kasaitaccen Majigin nan da aka nuna an Najeriya mai suna “The wedding party 2 Destination Dubai” a turance ya bayyana cewa fim din ya sami kudi sama da Naira Miliyan 73, a karshen makon da aka fara nun shi. An fara nuna fim dinne a gidajen kallon fina-finai ko Cinema a turance ranan 15, ga watan Disambar da muke ciki a fadin kasar.
A yanzu haka wannan fim shine ya fi kowane ciniki a kasuwar nuna fina-finai ta Najeriya inda kashi na farko ya sami zunzurutun kudi har Naira miliyan 36, a satin farko da aka fara nuna shi a shekarar data gabata.
Mo Abdu, babbar shugabar studiyon nan mai suna Ebony studio, kuma daya daga cikin furodusoshin fim din ce ta bayyana nasarar a shafinta na Instagram, inda ta rubuta cewa “babu abinda zan ce sai dai godiya ga ubanji. Da kuma ‘yan Najeriya”.
Fim din wedding Party 2 Destination Dubai, yanzu shine na farko da ya taba samu wadannan makudan kudade cikin satin farko da aka fara nuna shi a fina-finan Najeriya dana kasashen ketare. “shekarar data gabata mun sami zunzurutun kudi har miliyan 36, a karshen makon da muka fara nuna fim din, amma wannan karon mun sami nunki biyu, wannan na nuni da cewa zamu iya, lallai zamu iya, ya kamata mu hada hannu tare domin nuna ma duniya cewa lallai za a iya damawa damu a fagen fina-finai.
Masoya fina-finan Najeriya sun dade suna tsammanin fitowar kashi na biyu na wannan fim da aka yi dake nuna aurataiya tsakanin kabilu da aka fassara shi zuwa ga rayuwar aure ta zahiri.
Facebook Forum