Atletico Madrid ta kai karar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona gaban hukumar kula da wasannin kwallon kafa na duniya (FIFA) kan cewar Barcelona tana zawarcin dan wasanta Antoine Griezmann mai shekaru 26, da haihuwa, domin ta sayeshi a karshen kakan wasan bana.
Kungiyar ta kai karar ce saboda acewarta kungiyar ta Barcelona, bata bi hanyar da aka shinfida ba domin zawargci ‘yan wasa ba.
Atletico Madrid tace kungiyar ta Barcelona tana amfani da wasu dabaru kan neman dan wasan ta hanyan magana da jama'ar da suke tare dashi da kuma bin kan iyalan sa wato yan'uwansa domin su shawo kan dan wasan da ya koma kungiyar
Yin haka kuma Atletico Madrid tana ganin ya kauce wa dokokin FIFA na zawarcin ‘yan wasa
Ko kwana kin baya ma wata mujalla ta rubuto ciwar shugaba kungiyar ta Barcelona ya gana da yan'uwan Griezmann kan batun komawarsa Barcelona.
A kwanakin bayane Antoine Griezmann ya sabunta kwangilarsa a kungiyar ta Atletico Madrid zuwa karshen kakan wasanni na shekarar 2021-22.
Mai magana da yawun hukumar ta FIFA yace zasuyi binceke kan zargin da kungiyar ta Atletico tayi akan Barcelona domin gane gaskiya lamarin kafin su zantar da hukunci.
Facebook Forum