Wasu mata biyu daga kasar Liberia da wata kuma daga kasar Yemen da su ka yi gwagwarmaya da rashin adalci, da danniya da kuma iskanci da mata da karfin tsiya, sun sami lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a jiya Asabar da aka yi shagalinsa a Oslo babban birnin Norway.
Yayin da jama’a su ka mike don girmama Shuagabar Kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, da ‘Yar rajin tabbatar da zaman lafiya Leymah Gbowee da kuma ‘yar gwagwarmayar kare hakkin mata a Yemen Tawakkul Karman, sai aka mika masu kyaututtukansu a dandalin birnin Oslo da aka kawata shi sosai.
Shugaban Kwamitin bayar da lambar yoban ta Nobel, dan asalin Norway Thorbjoern Jagland ya gaya ma matan cewa sun zamanto darasi na gwagwarmayar kare hakkin bil adama musamman ma mata.