Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Aikin Yi Ya Karu A Kasashe Masu Karfin Tattalin Arziki


Wani ma'aikaci yake hawa wani sabon gini da ake aiki akansa.
Wani ma'aikaci yake hawa wani sabon gini da ake aiki akansa.

Har yanzu marasa aikin yi a kasashe da suka ci gaba yana da yawan gaske, wadda yake janyowa shugabanni rashin barci.

Har yanzu marasa aikin yi a kasashe da suka ci gaba yana da yawan gaske, wadda yake janyowa shugabanni rashin barci, akokari da suke yi na kaucewa wata koma bayan tattalin arzikin Duniya.

Alkaluma da kungiyar ci gaban tattalin arziki da ayyukan more rayuwa ta sake ya nuna cewa rashin aikin yi a fadin kasashe 34 dake cikin kungiyar, ya haura zuwa kashi 8.3 cikin watan Oktoba, daga kashi 8.2 cikin watan Nuwamba.

Kungiyar OECD tace adadin mutane da basu da aikin yi a kasashe da suke kungiyar mutane milyan 45 da dubu dari daya cikin watan Oktoba, galibin wan nan adadi a turai ne.

Yankin turai baki daya yaga rashin aikin yi ya haura zuwa kashi 10.3,wan nan shine kashi mafi yawa da ya taba gani tun lokacin da Duniya ta fuskanci koma bayan tattalin arziki.

Kasar Spain da Netherlands su suka ga karuwar rashin masu aikin yi, Andalusiyar (Spain) ta yawan wadanda basu da aikin yi ya kai kashi 22.8. Masu fashin baki suna fargabar matsalolin tattalin arziki da Spain take fuskanta zai tilastawa kasar ta hudu a girman tattalin arziki a yankin kasashe na Euro ta shiga sahun Girka da wasu kasashe d a suka nemi tallafin kasa da kasa domin magance matsalar da suke ciki.

Haka ma a alkaluma da aka sake cikin watan Nuwamba ya nuna rashin aikin yi ya ragu a Amurka, tattalin arziki mafi girma a Duniya da kamar kashi 0.4.

Aika Sharhinka

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG