Wasu Kasusuwa Sun Nuna Kasancewar Wata Dadaddiyar Al'uma Da Ta Shude!

Wasu daddadun kasusuwa da aka gano a kasar Canada, suna nuni da cewar akwai alamun halittun mutane a doron kasa da suka kai kimanin fiye da shekaru milliyan hudu, a cewar wani bincike da aka buga a jaridar halittu.

Duk a cewar masanan ba su iya gano takamaimain shekarun kasusuwan ba, harma suna ganin kamar suna iya wuce shekaru milliyan hudu da milliyan 3000 ko kuma kusa da hakan.

Ya zuwa yanzu dai babu wasu kasusuwa da aka taba samu da suka nuna alamun dadewa da ta kai wadannan a fadin duniya, a cewar Farfesa Dominic Papineau, na jami’ar College London wanda yake jagorantar binciken.

A cewar Farfesa Dominic, wannan binciken nasu ya kara bayyana musu cewar, jim kadan bayan kirkirar wannan duniyar mutane suka fara rayuwa a kai, wanda hakan ya kara tabbatar da shekarun wannan kasusuwan da suka kai shekaru sama da billiyan 4.5.

Kana akwai tabbacin mutane sun yi rayuwa a wata duniyar ruwa mai kama da wannan duniyar na kankanin lokaci.

Muna sa ran gano alamun rayuwa a duniyar wata da suka kai shekaru billiyan hudu da suka wuce, in ji Fafesa Papineau.