Wasu Jihohin Najeriya Za Su Soma Bita Da Sabunta Dokoki Don Baiwa Sarakuna Damar A Dama Da Su

Wani taron Sarakunan gargajiya a Najeriya

A Najeriya sarakunan gargajiya sun jima suna korafi akan ba su da wani tanadi na aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su wanda za su bayar da gudunmowa ga ci gaban al'umar kasa.

Sai dai yanzu wannan matsalar ta soma samun kulawa, domin mahukuntan wasu Jihohin kasar sun soma tunanin bita da sabunta dokokin Jihohin da za su hada da baiwa sarakuna gurbi a ciki,domin su bayar da gudunmuwa ga kyautata rayukan jama'ar su.

Samarwa tare da yin biyayya ga dokokin kasa sahihiyar hanya ce ta kyautata rayuka da sauran al'amurra ta yadda komai zai gudana yadda ya kamata a kasar.

To sai dai saboda rashi ko kuma dadewa ba'a yi bita da sabunta wasu dokoki ba, ana samun rashin ci gaba da kawo rauni ga tafiyar wasu lamurra cikin nasara.

Bisa ga la'akari da hakan ne ya sa mahukuntan wasu Jihohi kamar na Sakkwato dake Arewa maso Yammacin kasar suka ga ya dace suyi bitar dokokin Jihohin su ciki har da baiwa sarakuna dama su bayar da gudunmuwa ga jama'a a hukumance.

Jama'ar kasar dai na ganin cewa wannan batun ya dace domin tsarin mulkin kasar bai ce komai ba akan sarakuna duk da muhimmancin dake gare su a cikin al'umma.

Bayan wannan dokar, akwai dokoki da yawa da gwamnatin ta yi bita aka sabunta su domin su tafi daidai da zamani.

A haujin masu fafatuka akan ganin an samu kyautatattuwar rayukan jama'ar kasa kuwa aiwatar da dokokin ne kadai zai nuna tasirin su ga jama'a.

Masu fashin baki akan lamurran yau da kullum na ganin da Jihohin Najeriya musamman wadanda ke makwabtaka da juna zasu rika hada hannu wurin dauka da kuma aiwatar da dokoki da za'a fi aiwatar da su yadda ya kamata kuma tasirin su zai fi amfani ga ‘yan kasa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Jihohin Najeriya Za Su Soma Bita Da Sabunta Dokoki Don Baiwa Sarakuna Damar A Dama Da Su