Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gombe: An Yi Sulhu Tsakanin Gwamna Inuwa Yahaya Da Sanata Danjuma Goje


Sanata Goje, hagu, gwamna Inuwa Yahaya, dama (Facebook/Isma’ila Uba Misilli
Sanata Goje, hagu, gwamna Inuwa Yahaya, dama (Facebook/Isma’ila Uba Misilli

Wannan sulhun na zuwa ne bayan da aka kwashe watanni ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin biyu, lamarin da a wasu lokuta ya kai ga fito na fito tsakanin magoya bayansu.

Kwamitin sulhu na Jam’iyyar APC na kasa ya gana da Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da tsohon gwamna Sanata Danjuma Goje a Abuja a wani mataki na samar da masalaha kan rashin fahimta da ke tsakaninsu.

Wata sanarwa da Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, ta ce taron ya gudana ne na karkashin jagorancin shugaban kwamitin tsare-tsare na rikon kwaryan jam’iyyar APC na kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni da sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka hada da tsohon kakakin majalisar wakilai Hon. Yakubu Dogara da Sanatoci da tsoffin gwamnoni.

Manyan 'yan jam'iyyar APC da suka sasanta Gwamna Inuwa Yahaya da Sanata Goje (Facebook/ Isma’ila Uba Misilli)
Manyan 'yan jam'iyyar APC da suka sasanta Gwamna Inuwa Yahaya da Sanata Goje (Facebook/ Isma’ila Uba Misilli)

“An baiwa Gwamna Inuwa Yahaya da Sanata Danjuma Goje damar gabatar da matsayarsu kan yadda rashin fahimta da rigingimu da ake ganin suna faruwa a Jam’iyyar APC a Jihar Gombe.” In ji Misilli.

Sanarwar ta kara da cewa, “an kuma gudanar da tattaunawa mai karfi da nufin warware matsalolin da ke faruwa, da kuma yadda za a samar da mafita tare da warware matsaloli da ɗinke duk wata baraka a cikin jam’iyyar a jihar gabanin babban taron jam'iyyar na kasa da shirye-shiryen babban zabe na 2023 dake tafe.”

“Wannan taro dai ci gaba ne na wanda aka yi tun farko a Gombe, inda kwamitin Abdullahi Adamu ya tattauna da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da sauran manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, da nufin magance korafe-korafe da rashin jituwa da suka taso daga zabukan jam'iyyar da aka kammala a jihar kwanan nan.”

Wannan sulhun na zuwa ne bayan da aka kwashe watanni ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin biyu, lamarin da a wasu lokuta ya kai ga fito na fito tsakanin magoya bayansu.

Sanata Goje ya mulki jihar ta Gombe tsakanin 2003 zuwa 2011.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG