Wannan Soki Burutsu ne Jama'a Basu Bukatar Hutu Wajen Taron Janar Buhari

Ziyarar John Kerry Zuwan Najeriya.

An tsaurara matakan tsaro da kuma bada hutu a ranakun Laraba da Alhamis.

An tsaurara matakan tsaro da kuma bada hutu a ranakun Laraba da Alhamis, a jihar Adamawa, domin karrama mayan ‘yan takarar shugaban kasa, a Najeriya, wato shugaba, Goodluck Jonathan da janar Muhammadu Buhari.

Tun farko dai an shirya cewa yau Laraba ne ake sa ran dan takarar, jam’iyyar adawa ta APC, janar Muhammadu Buhari, sai sauka a jihar ta Adamawa, yayi da shi kuwa Goodluck Jonathan, sai gobe alhamis.

Awowi kadan da bayyana wannan mataki da Gwamnati jihar da dauka sai ga wata sanarwa daga jam’iyyar APC, na bayyana cewa an dage zuwan Buhari, tare kuma da nisanta kanta da wannan matakin da Gwamnatin jihar Adamawa ta dauka na bada hutu.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar ta APC, Reverend Pinas Padiyo, Yace " Karramawa janar Buhari, ne akayi muka nemi, abamu dandalin Ribadu, dake tsakirar birnin Yola, aka hana mu, wannan soki burutsu ne da zamba cikn aminci zamu kira shi ake so ayiwa jama'ar, Adamawa, babu wani abu wai karrama dan takarar mu wai abada hutu, jama'a basu bukatar hutu wajen taron janar Buhari."