Shugaban majalisar malamai na kungiyar reshen Abuja Sheikh Ibrahim Duguri shi ya bayyana hakan a wa'azin kasa da aka yi a Abuja karshen mako.
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir yayi kira a tunkari zaben cikin lumana. Yace addinin musulunci rayuwa ce gaba daya ciki kuma har da siyasa. Kowa ya je yayi zaben domin Allah ba domin kwadayin abun duniya ba. Su lura da cancanta da yadda za'a maido da tsaro kasar da cigaban bunkasar ilimi da tattalin arziki. Yace duk wadannan ba zasu yiwu ba sai an lura da cancanta. Duk wani dan siyasa kuma da ya fito a duba tarihinsa. Kada a yi wasa da kuri'a.
Ya yabawa INEC da tace ta shirya ta gudanar da zaben domin a wanan karon adadin wanda suka yi ragista sun fi wadanda suka yi zabe a shekarar 2011.
Kungiyar ta kira kada kowa ya bari a zolayeshi yayi fada. Gyara a ke bukata ba fada ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya domin karin bayani.