Wani Tsohon Madugun ‘Yan Tawayen Nijar Ya Kaddamar Da Wani Yunkuri Na Yakar Sojojin Da Su Ka Yi Juyin Mulki

Kwamandan tsofuwar kungiyar ‘yan tawayen Arewacin jamhuriyar Nijar Rhissa Ag Boulla

Wani tsohon madugun 'yan tawaye kuma dan siyasa a Jamhuriyar Nijar ya kaddamar da wani yunkuri na fafatawa da sojojin da su ka yi juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli, lamarin da ke zama wata alama ta farko ta adawar cikin gida da mulkin soja a wannan kasa mai matukar muhimmanci a yankin Sahel.

WASHINGTON, D.C. - Rhissa Ag Boula ya fada a cikin wata sanarwa da aka gani a yau Laraba cewa, sabuwar kungiyar mai suna Majalisar Gwagwarmayar Jamhuriya (CRR) tana da nufin mayar da hambararren Shugaban kasar Mohamed Bazoum, wanda ke tsare a gidansa tun bayan da aka karbe mulki.

Sanarwar ta ce "Nijar ta fada cikin wani bala'i daga mutanen da aka basu amanar kare kasa."

Kaddamar da shirin na zuwa ne a dai dai lokacin da yunkurin diflomasiyya na neman kawo karshen juyin mulkin ya ci tura bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi watsi da sabuwar tawagar diflomasiyya, da kuma gwamnatocin sojojin kasashen Mali da Burkina Faso da ke makwabtaka na goyon juyin mulkin, inda suka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta hana duk wani yunkuri na soji.

Da yake maida martani dangane da kafa wannan kungiyawani dan asalin yankin arewacin Nijer shugaban jam’iyarPNPD AKAL KASA Intinicar Alhassan ya ce bai yi mamakinjin irin wannan barazana daga wajen Rhissa AG Boulla ba.

Jagororin juyin mulkin jamhuriyar Nijar sun hana jakadun kasashen Afirka da na Majalisar Dinkin Duniya shiga kasar a ranar Talata, inda suka yi watsi da matsa masu cewa su shiga tattaunawa gabanin taron da za a yi ranar Alhamis, inda shugabannin kungiyar ECOWAS za su tattauna kan yiwuwar amfani da karfi.

Wani mamban CRR ya ce wasu jiga-jigan siyasar Nijar da dama sun shiga kungiyar amma ba za su iya bayyana kansu a bainar jama'a ba saboda suna tsoro.

Ag Boula ya taka rawa a tayar da kayar bayan da Abzinawa su ka yi. Abzinawa ‘yan wata kabila ce ta makiyaya da ta kasance a Arewacin hamadar Nijar, a shekarun 1990 da 2000. Kamar sauran tsoffin ‘yan tawaye, an shigar da shi cikin Gwamnati karkashin Bazoum da magabacinsa Mahamadou Issoufou.

Yayin da ba a san iyakar goyon bayan CRR ba, furucin Ag Boula zai zama abin damuwa ga jagororin juyin mulkin ganin yadda ya yi tasiri a tsakanin Abzinawa, wadanda ke rike da harkokin kasuwanci da siyasa a mafi yawan yankunan Arewacin kasar. Goyon bayan Abzinawa abu ne mai muhimmanci wajen ganin ikon sojojin da su ka yi juyin mulki ya zarce birnin Yamai.

Majalisar Dinkin Duniya, da kasashen Yammacin duniya da kuma kasashe mambobin ECOWAS na dimokuradiyya irinsu Najeriya na son gwamnatin mulkin soja ta maido da Gwamnatin farar hula da ta yi nasarar dakile munanan hare-haren masu da’awar kishin Islama da suka addabi yankin na Sahel.

-Reuters

Saurari karin bayani daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Tsohon 'Dan Tawayen Nijar Ya Kaddamar Da Yunkurin Sake Juyin Mulki Daga Hannu Sojoji .MP3