Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Na Fuskantar Karin Takunkumi


Shugaban ECOWAS kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban ECOWAS kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

An kakabawa Nijar karin takunkumi, sa'o'i bayan da sabbin shugabannin sojin kasar suka yi watsi da sabuwar tawagar diflomasiyya da nufin maido da tsarin mulkin kasar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin sanya sabbin takunkuman ta hannun babban bankin Najeriya, da nufin matsin lamba ga masu hannu a cikin lamarin, inji mai magana da yawun shugaban kasar.

Hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)
Hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)

An dai kakabawa Nijar takunkumin ne bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta hana tawagar hadin gwiwa daga kasashen yammacin Afirka da kungiyar Tarayyar Afirka AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya izinin shiga kasar, yayinda suka yi watsi da matsin lamba daga Amurka da Majalisar Dinkin Duniya na neman a zauna teburin tattaunawa.

Da yammacin jiya Talata ne kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta tabbatar da cewa, kokarin samun masalahar da aka yi na hadin gwiwa ya faskara, ta kuma bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin maido da tsarin mulki a Nijar.

Mahukuntan yankin da na yammacin Afirka na fargabar juyin mulkin zai dagula al'amura a yankin Sahel na yammacin Afirka, daya daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya da tuni ke fama da juye-juyen mulki da kuma mummunar tada kayar baya na Islama.

Rufe kan iyaka da na sararin samaniya ya katse hanyoyin samar da magunguna da abinci, lamarin da ke kawo cikas ga tallafin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya. Haka kuma manufofin Amurka da na kasashen Yamma a Nijar, wadda tsohuwar kawarta, na fuskantar barazana.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa, "Har yanzu muna da bege kuma muna ci gaba da kokarin cimma sakamakon da zai koma ga tsarin mulkin kasar."

Matthew Miller
Matthew Miller

Ba da tallafin ilimi da horar da sojoji na kasa da kasa, ayyukan wanzar da zaman lafiya, da kuma shirye-shiryen bayar da tallafin sojojin kasashen waje da ke taimakawa Nijar wajen yaki da ta'addanci na daga cikin taimakon da Amurka ta dakatar tun bayan juyin mulkin.

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS na shirin gudanar da wani taro a yau Alhamis domin tattaunawa kan rikicin da ke tsakaninsu da gwamnatin mulkin soja, da ta ki amincewa da wa’adin da aka ba ta a ranar 6 ga watan Agusta na maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Shugabannin kungiyar ECOWAS sun amince a makon da ya gabata da wani shiri na daukar matakin soji, wanda ake sa ran shugabannin kasashen za su duba a taron da suke yi a Abuja babban birnin Najeriya.

Duk da haka, mai magana da yawun Tinubu ya ce shugabannin sun gwammace su bi ta hanyar diflomasiyya.

~ REUTERS

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG