Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Nada Sabon Firai Ministan Gwamnatinsu


Ali Mahaman Lamine Zeine Firai Ministan Gwamnatin rikon kwarya na Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar
Ali Mahaman Lamine Zeine Firai Ministan Gwamnatin rikon kwarya na Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar

Sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijer sun nada Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin Firai Ministan Gwamnatin rikon kwaryar da suke shirin kafawa a dai dai lokacin da karamar sakatariyar Amurka mai kula da harakokin siyasa Victoria Nuland ta kai ziyara a Nijar.

NIAMEY, NIGER - Sakatariyar kula da harkokin siyasar ta Amurka ta kai ziyara ne da nufin share fagen sulhunta bangarorin da ke takaddama sanadiyyar juyin mulkin da soja suka yi wa zababben Shugaban kasa Mohamed Bazoum.

Har ya zuwa jiya litinin 7 ga watan Agusta, Ali Mahaman Lamine Zeine shi ne wakilin bankin BAD kokuma ADB a Chadi. Jigo a jam’iyar MNSD Nassara, sabon Firai Ministan na Gwamnatin mulkin sojan ta Nijar an haife shi ne a 1965 a Zinder.

Zeine ya rike mukamin darektan fadar Shugaban kasa a zamanin marigayi Shugaba Tanja Mamadou a shekarar 2001 kafin daga bisani aka nada shi Ministan kudin kasa a shekarar 2003.

Ya karanci harakokin kudi da hada-hadar banki a cibiyar CEFEB ta birnin Marseille na kasar Faransa inda ya fito da digiri na uku. A cewar shugaban kungiyar Voix des sans Voix, Nassirou Saidou nadin Zeine abin farin ciki ne a bisa wasu dalilai.

Shirin kafa gwamnatin ta rikon kwarya na gudana a wani lokacin da Amurka ta kaddamar da shirin samar da hanyoyin warware kullin da ya sarke a Nijar mafarin aiko da karamar Sakatariyar Gwamnati Victoria Nuland zuwa Yamai.

Ta ce “muna so mu yi magana ta gaskiya da masu hannu a wannan al’amari na kalubalen da dimokradiyya ke fuskanta don mu san ko zai yiwu mu zakulo hanyoyin warware wannan kiki-kaka ta hanyar diflomasiya”.

Victoria Nuland ta ce sun gana da hafsan hafsohi Janar Moussa Salao Barmou don sanar da shi abinda ke tafe da ita sai dai an fuskanci turjiya dangane da ainahin abinda ake fatan ganin an cimma.

Ta kara da cewa “kafin mu iso mun bukaci a ba mu damar ganawa da Shugaba Bazoum don mu yi magana da shi gaba da gaba mu ji ta bakinsa game da mafitar wannan al’amari amma ba mu samu ganinsa ba. Haka kuma mun bukaci a dauki matakin inganta yanayin rayuwa a inda suke tsare da dansa da matarsa domin suna cikin mawuyacin halin rayuwa”.

Ta ce “sannan ba a bamu damar ganin Tchiani ba wato Shugaban sojojin da suka yi juyin mulkin to amma mun yi magana da Barmou, a game zahirin matsayinmu a wanna al’amari”. Aiki ne mai wuya amma kuma wanda ke da mahimmanci sosai wajen magance sarkakiyar da aka shiga.

Wata tawagar hadin gwiwar jami’an Gwamnatocin mulkin sojan Mali da Burkina Faso ta yi rangadi a nan Yamai da yammacin jiya domin bai wa takwarorinsu na Nijar goyon baya a wannan lokaci da kasashen duniya suka sa su gaba sanadiyyar yi wa dimokradiyya karan tsaye.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Nada Sabon Firai Ministan Gwamnatinsu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG