Farmakin Sojin Isra'ila A Khan Younis Ya Hallaka Mutane 20

Khan Younis a Kudancin Gaza bayan harin da Isra'ila ta kai

A yau Laraba tankokin yakin Isra’ila suka matsa zuwa yankunan arewacin Khan Younis dake kudancin zirin Gaza kuma jami’an bada agajin Falasdinu sun ce hare-haren Isra’ilar ta sama sun hallaka akalla mutane 20 a fadin zirin

Mazauna yankin sun ce tankokin sun matsa ne kwana guda bayan da rundunar sojin Isra’ila ta bada sabon umarnin kwashe jama’a, inda suka ce an harba rokoki daga yankin.

Khan Younis a kudancin Gaza

Ganin kwanson harsashai na sauka a kusa da unguwannin zaman mutane, yasa iyalai barin gidajensu tare da nausawa yamma zuwa yankin al-mawasi da aka ayyana a matsayin tudun mun tsira dake kusa.

A cewar jami’an bada agaji, an hallaka mutane 11 a hare-hare 3 ta sama da aka kai yankunan tsakiyar Gaza, ciki harda yara 3 da wani jami’in bada agaji. Biyar daga cikin wadanda aka kashe na bin layi ne a wajen wani gidan biredi, a cewarsu.

Haka kuma hare-haren igwa sun hallaka Falasdinawa 9 a yankin Rafah, dake kusa da kan iyakar Masar, a cewar jami’an bada agajin.

Rundunar sojin Isra’ila bata yi martani nan take akan rahoton jami’an bada agajin ba.

Dakarun Isra’ila sun yi luguden wuta akan asibitin kamal Adwan dake yankin Beit Lahiya na arewacin Gaza kwanaki 5 a jere, a cewar shugaban asibitin Hussam Abu Safiya, inda yace an raunata 3 daga cikin ma’aikatansa a daren jiya Talata, kuma guda yana cikin mawuyacin hali.

Khan Younis a kudancin Gaza

“Jiragen sama marasa matuka na jefo bama-bama dake raunata duk wanda ya motsa,” a cewar Abu Safiya. “halin da ake ciki na bukatar daukin gaggawa.”

Mazauna garuruwa 3-Jabalia da Beit Lahiya da Beit Hanoun-sun ce dakarun Isra’ila sun tarwatsa gidaje da dama.

-Reuters