Daga cikin wadanda suka mutu a sansanin 'yan gudun hijiran Nuseirat da kuma sansanin 'yan gudun hijiran Bureij, akwai yara uku da mace guda, a cewar kungiyoyin agajin gaggawa na Falasdinawa da suka kai gawarwakin zuwa asibitin Al-Aqsa Martyrs da ke kusa. 'Yan jaridan AP sun kirga gawarwakin mutane 13 a asibitin.
Mace macen baya-bayan nan na zuwa ne adaidai wani lokaci da ake bege gani a yakin da ya addabi Gaza, bayan da tawagar likitocin suka ceto jariri da rai daga wata mace Bafalasdina mai juna biyu da aka kashe a harin na jirgin sama da ya fada kan gidanta da ke Nuseirat da yammacin ranar Alhamis.
An kashe Ola al-Kurd mai tsohon ciki mai shekaru 25 tare da wasu mutane 6 a tashin bam din, amma jami’an agajin gaggawa suka garzaya da su asibitin Al-Awda da ke arewacin Gaza da fatan ceto yaron da ke cikinta. Sa'o'i kadan bayan haka, likitoci sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa an haifi yaron.
Jaririn da har yanzu ba a rada masa suna ba yana cikin koshin lafiya, sai dai yana fama da karancin iskar oxygen kuma an sanya shi a cikin na’urar incubator, in ji Dr. Khalil Dajran. Mahaifin yaron ya samu rauni a wannan harin, amma ya tsira da ransa.
Yakin na Gaza, wanda ya barke sanadiyar hari da Hamas ta kai wa kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 38,900, a cewar ma'aikatar lafiyar yankin, wadda ba ta banbance tsakanin mayaka da fararen hula a kidayar ta. Yakin ya haifar da bala'in jin kai a yankin Palasdinawa da ke gabar teku, inda aka raba mafi yawan al'ummarta miliyan 2.3 da muhallansu tare da janyo yunwa mai yawa.
Harin na Hamas a watan Oktoba ya kashe mutane 1,200, galibi fararen hula, sannan mayakan sun yi garkuwa da kusan mutane 250. Kimanin mutane 120 ne suka rage a hannu ake garkuwa da su, inda aka yi imanin kusan kashi uku daga cikinsu sun mutu, a cewar hukumomin Isra'ila.
Dandalin Mu Tattauna