Wani ayarin shugabannin Afirka na kan hanyarsa zuwa Ivory Coast a wani yinkurin shawo kan Laurent Gbagbo ya sauka

Firai Ministan kasar Kenya Raila Odinga (L) da Gilbert Ake, Firai Ministan gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo, Abidjan, 03 Jan 2011.

Wani ayarin shugabannin Afirka na kan hanyarsa ta zuwa Ivory Coast a wani yinkurin na shawo kan bijirarren shugaba mai ci Laurent Gbagbo ya sauka.

Wani ayarin shugabannin Afirka na kan hanyarsa tzuwa Ivory Coast a wani yinkurin na shawo kan bijirarren shugaba mai ci Laurent Gbagbo ya sauka.Firayim Ministan Kenya Raila Odinga ya isa Abidjan babban birnin kasar yau Litinin. An jima kuma shugaban Benin, da Cape Verde da Sierra Leone za su bi sahu.Wasu jami’an Tarayyar Afirka da na kungiyar kasashen Yammacin Afirka ECOWAS sun ce shugabannin za su yi kokarin shawo kan shugaba Gbagbo ya sauka salin alin a wani yanayin da za a tabbatar da tsaron lafiyarsa.Kungiyar ta ECOWAS dai ta yi barazanar korar Gbagbo karfi da yaji muddin ya ki mikawa Alassane Ouattara ragamar iko. Tarayyar Turai, da kungiyar ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya duka sun ayyana Mr. Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba da kuma kasancewa sabon Shugaban Ivory Coast.Mr. Gbagbo ya ce shi ya ci zaben kuma ya ki mika ragamar iko.