Shugabannin Afirka na ci gaba da daukan matakan diflomasiyya domin warware matsalar siyasar zaben shugaban kasa dake addabar kasar Ivory Coast cikin lumana, a dai dai lokacin da jami’an rundunar sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya ke cewa suna binciken ayyukan cin mutumcin Bil Adama da ake zargin ana tafkawa a Ivory Coast.
Friministan kasar Kenya Raila Odinga, zai hadu da sauran shugabannin kasashen Benin, da na Sierra Leone da Cape Verde, wani lokaci a yau litinin domin tattaunawa da shugaban dake kan gado na yanzu, Laurent Gbagbo.
Mr. Odinga, shine wakilin tarayyar Afirka dake shiga tsakani a rikicin siyasar Ivory Coast.