Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan sanda a jihar Bauchi sun ce sun bankado wata makarkashiyar kaiwa wata majami’a harin bom


Harin Bom a Najeriya.
Harin Bom a Najeriya.

Yan sanda a jihar Bauchi sun ce sun bankado wata makarkashiyar kai hari bom kan wata majami’a dake babban birnin jihar

Yan sanda a jihar Bauchi sun ce sun bankado wata makarkashiyar kai hari bom kan wata majami’a, kwanaki bayan kazamin rikicin da aka yi takanin Musulmi da Kirista a jihar. Hukumomi sun ce wani mutum ya shiga da nakiya cikin majami’ar Methodist dake cikin garin Bauchi lokacin da ake sujada ranar Lahadi da safe da ake samun cunkoson jama'a. Jami’an tsaro sun sami labarin shirin kai harin. Kwararru a fannin tarwatsa bom suka fitar da bom din daga majami’ar suka tarwatsa shi a waje ba tare da yayi barna ba. Jihar Bauchi tana makwabtaka da Plateau inda mutane da dama suka mutu a rikicin addini da na kabilanci cikin watannin da suka shige. Mazauna jihohin Bauchi da kuma Plateau suna zama cikin fargaba na tsawon makonni, yayinda hukumomi ke kokarin shawo kan tashe tashen hankulan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG