Shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan zai kai ziyara kudancin Sudan wani lokaci a yau Talata, mako guda kafin zaben raba gardama da ake ganin zai kawo rabuwar kasar Sudan wadda tafi kowace girman kasa, a nahiyar Afirka.
Wani babban jami’in jam’iyyar dake mulkin kasar Sudan,Rabie Abdelati Obeid, yace a lokacin ziyarar, shugaba Omar al-Bashir zai tattauna tare da shirin samun nasarar kuri’ar raba gardamar,sannan ya saurari korafe-korafen shugabannin yankin kudanci tare da basu tabbacin gudanar da zaben raba gardama cikin ‘yanci da walwala.
Obeid yace shugaban na Sudan zai kokarta tabbatarwa al’ummar kudancin Sudan niyyar Gwamnatinsa ta inganta dangantaka koda kuwa kada kuri’ar amincewa ballewa daga tarayyar kasar Sudan.
Tsohon shugaban Amirka Jimmy Carter, da tsohon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan,sune zasu jagorancin tawagar jami’an kasa da kasa sama da dari domin nazartar shiirn kuri’ar raba garadamaar.