Wakar wata kafa ce ta mika sakonni ga alumma kan harkokin rayuwa, inji wani matashin mawaki Siwudi Inuwa. Yace yana amfani da wakar wajen isar da sakonni na abubuwan da suka faru ne domin ya kasance ishara ga na baya.
Ya bayyana haka ne ayayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA, Baraka Bashir, a birnin Kano, matashi yace yana da wata sana’ar hannu da nake yi bayan harkar waka, kuma kamar kowannen mawaki “ ina waka ne domin isar da sako ga alumma”.
Ya ce, da dama wakokinsa na karkata ne na dabi’un alumma mussaman ma dangogin soyayya da cin amana da mafi yawa mata kanyi wa samarin da basu da abin hannu.
Ya ce yana wakokin yabo sannan kuma yakan rera waka idan wani abu ya afku da shi, inda yake bada misalin da wata waka da ya rera mai suna bakar kunama, inda aka hana shi aure tare da soyayya ga wata masoyarsa sakamakon rashin abun hannu, haka zalika ita budurwa ta ki shi sakamakon hakan.
Ya kara da cewa manufarsa ya nusar tare da nishadantar da masu sauraronsa, walau a kansa ko waninsa.
Your browser doesn’t support HTML5