Kungiyar kwallon kafa ta Nigeria Super Eagles ta lallasa ta kasar Argentina, daci 4-2 a wasan sada zumunta da akayi ranar Talata a Krasnodar na kasar Russia,
Kasar Argentina ita ta fara jefa kwallon a ragar Najeriya a cikin minti na 27 da fara wasa ta kafar dan wasanta E.Banega, sai kuma Sergio Aguero a minti na 36.
Najeriya ta samu damar jefa kwallonta na farko ne ta kafar Kelechi Iheanacho, a mint na 44, daga bisani bayan an dawo daga hutun rabin lokaci dan wasan gaban Najeriya, Alex Iwobi, ya jefa kwallo ta biyu, a minti na 52 sai Bryan Idowu, ya sake saka kwallo ta uku a ragar Argentina, ana mintui na 73 sai Alex Iwobi ya sake zurara kwallo ta hudu, haka dai aka tashi a wasan.
Sai dai shahararen dan wasan gaba na Argentina Lionel Messi bai samun damar fafata a wasan ba.
A bangaren Najeriya kuwa ita ma dan wasanta Victor Moses bai samu damar fafatawa a wasan ba sabo da wasu dalilai.
Wannan shene karo na tara da kasashen ke haduwa a tsakaninsu, inda kasar Argentina tayi nasara sau biyar akan Nigeria,
Ita kuma Nigeria sau uku take nasara akan Argentina anyi kunnen doki sau daya.
A shekara 1994 Argentina ta doke Najeriya 2-1 sai 1995 akayi canjaras 0-0, 1996 Najeriya ta doke Argentina 3-2 a 2002 Argentina ta yi nasara akan Najeriya 1-0, a 2010 Argentina ta sake samu nasara akan Najeriya, da ci 1 da 0, a 2011 Najeriya ta lallasa Argentina, 4 da 1.
Har ila yau 2011 Argentina 3-1 Najeriya, 2014 Argentina 3-2 Najeriya, sai kuma a bana 2017 Najeriya ta doke Argentina da kwallaye 4-2.
Facebook Forum