Kungiyar masu shirya fina finai watau MOPPAN, tace hbar yanzu bata yanke shawara akan afuwar da Rahama Sadau, ta nema da kungiyar ba sakataren kungiyar Muhammad Salisu Ofisa ne ya bayyana a lokacin da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir ta zanta da shi kan batun neman afuwa da jaruma Rahama Sadau ta yi.
Sakataren ya ce tabbaci hakika Rahama, ta rubuto takardar neman afuwa amma abune da ya shafi rssa daban daban saboda haka ba kungiyar daya bane zata yanke hukunci sai rassa da abun ya shafa sun zauna sannan za a yanke hukunci akai.
DandalinVOA ya kuma tambaye Muhammad Salisu Ofisa ko me ke kawo jinkiri wajen aiwatar da yanke hukunci sai ya ce, dole sai mutane da suka zartar da wancan hukunci sun zauna gaba daya sannan ne za’a yanke hukunci, bayan an duba takardar da ta rubutu.
Ya kara da cewa har yanzu suna fuskantar matsalolin satar fasaha, rashin kudi da kuma rashin zuba jari daga wasu sasssan mutane , tare da rokon gwamnatin wajen hada karfi da karfe domin magance wadannan matsaloli.
Facebook Forum