Wakilan kungiyar ECOWAS zasu sake komawa Ivory Coast makon gobe

Shugabannin Afrika ta kudu suna ganawa da shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo a Abidjan, 28 Dec 2010, daga hagu zuwa dama; Benin shugaba Boni Yayi, Cape Verde shugaba Pedro Pires, Sierra Leone shugaba Ernest Bai Koroma

Wakilan kungiyar ECOWAS zasu sake komawa Ivory Coast makon gobe

Shugabannin kasashen yammacin Afirkan nan uku zasu koma Ivory Coast makon gobe domin matsawa shugaba Laurent Gbagbo lamba ya mika mulki ga mutumin da kasashen Duniya suka yarda cewa shine ya lashe zaben kasar da aka yi cikin watan jiya. Shugaban kasar Benin,Cape Verde da saliyo duk sun gana jiya Talata da shugaba Gbagbo inda suka bukaci ya amince da sakamakon zaben da aka yi cikin watan jiya.Amma sun bar Ivory Coast yau laraba ba’ atareda an cimma matsaya ba,zuwa Abuja inda suka gana da shugaba Goodlcuk Jonathan na Najeriya,wanda ahalin yanzu shine shuagban kungiyar ECOWAS.Tawagar ta kuma gana jiya talata da Allassane Quattara, mutumin da aka hakince shine ya lashe zaben.