Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta ce hukumar za ta "tattauna tare da manyan masu ruwa da tsaki kan a wannan sabuwar dambarwa da ke faruwa" a Togo gabanin zaɓen 'yan majalisar dokoki da na yanki a ranar 29 ga Afrilu.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, tawagar zata samu jagorancin Maman Sambo Sidikou, tsohon shugaban tawagar Tarayyar Afirka a Mali da Sahel. Zai ci gaba da zama a kasar har zuwa ranar 20 ga Afrilu bayan gayyatar da gwamnati ta yi masa.
Tun a watan jiya ne ake zaman doya da manja a kasar Togo, lokacin da 'yan majalisar dokokin kasar suka goyi bayan sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar wanda zai kai kasar ga tsarin da zai ba majalisar dokoki hurumin zaben shugaban kasa na tsawon shekaru shida.
'Yan adawar dai na fargabar cewa wata dabara ce ta tsawaita wa'adin mulkin Gnassingbe, wanda ke kan karagar mulki tun shekara ta 2005, kuma ya yita sake lashe zabe a kuri'u da dama da 'yan adawa suka yi Allah wadai da su a matsayin magudi.