Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Dakatar Da Tantance Takardun Shaidar Digirin Jami’o’in Benin Da Togo


Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

Ma’aikatar Ilimin Tarayyar Najeriya ta dakatar da aikin tantance shaidar karatun digirin jami’o’in Jamhuriyar Benin da Togo har sai ta kammala wani bincike.

Dakatarwar da ta soma aiki tun daga ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2024 na da nasaba da wani binciken baya-bayan nan mai taken: “binciken kwakwaf akan yadda wakilin mujallar “Daily Nigerian” ya samu shaidar digirin wata jamai’a a Kwatano cikin makwanni 6 harma ya fara aikin hidimar kasa”.

A cewar Ma’aikatar Ilmin Najeriyar binciken zai shafi Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya da kuma kasashen 2, harma da ma’aikatun ilmin kasashen 2 da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS da kuma Hukumar Kula da Aikin Hidimar Kasa ta Najeriya.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta Ma’aikatar Ilimin Tarayyar Najeriya, Mrs. Agustina Obilor-Duru ta bayyana cewar, “an ja hankalin ma’aikatar ga wani aikin binciken kwakwaf na ‘yan jarida daya kai ga jaridar “Daily Nigerian” wallafa wani labari a ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2023 mai taken: “ binciken kwakwaf akan yadda wakilin jaridar daily nigerian ya samu shaidar kammala karatun digiri cikin makwanni 6 harma ya shiga aikin hidimar kasa”.

Jami’ar ta kara da cewar, “a ko da yaushe ana amfani da tsarin da duniya ke bi wajen tantance takardun shaidar kammala karatu wanda ke ta’allaka akan samun jadawalin kwasakwasan da cibiyoyin ilmi ke gudanarwa a kasashen duniya daban-daban”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, ma’aikatar ta kuma fara gudanar da nata bincike domin tantance ko akwai hannun jami’anta a lamarin, inda zata yi amfani da dokokin aikin gwamnati wajen hukuntasu.

Sanarwar ta yi nuni da cewa ma’aikatar da Hukumar Jami’o’i ta Kasa NUC sun yi gargadi game da shiga irin wadannan cibiyoyi, a wasu lokutan a baya baya, kuma akwai bukatar al’umma su rinka kai rahotanni irin wadannan ga jami’an tsaro domin dakile masu aikata laifuka.

Dangane da batun, ma'aikatar ta yi alkawarin sake duba dabarunta, da karfafa hanyoyin, da kuma yanke hukunci kan duk wani jami'in da ke da hannu a ciki.

Ma’aikatar ta jaddada kudirinta na tabbatar da daidaito a duniya, ta kuma baiwa ‘yan Najeriya tabbacin ci gaba da kokarin tsaftace fannin ilimi, tare da hana neman takardar shaidar boge ta digiri—na gida da waje.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG