WASHINGTON, D. C. - Dalibar mai suna Nabeeha Al-Kadriyar, ‘yar shekaru 21, ta kasance mai "kirki da kaifin basira," kamar yadda 'yar uwarta Asiya Adamu ta shaida wa BBC a ranar Litinin.
Kuma Nabeeha tana sha'awar rubuta wakoki da karanta littafan marubuciyar nan Ba’amurkiya Jodi Picoult, kuma kwanaki kadan ya rage da ta kammala karatun digiri a fannin kimiyya a jami'ar Ahmadu Bello.
Da yammacin ranar 2 ga watan Janairu ne aka sace Nabeeha tare da mahaifinta da ‘yan uwanta mata daga gidansu da ke wajen babban birnin tarayya Abuja.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta tabbatar da abin da ya biyo baya ba, amma shaidu sun ce kawun Nabeeha ya ruga ya nemi agaji sai wasu suka yi kwanton bauna suka kashe shi, tare da wasu ‘yan sanda uku. Ba a san dalilin da ya sa aka kai wa iyalin hari ba.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su makudan kudade nan da ranar 12 ga watan Janairu, kuma da basu samu ba sai suka kashe Nabeeha a matsayin gargadi, kamar yadda wani dan gidan ya shaida wa BBC, amma ya bukaci a sakaya sunan sa.
Wadanda suka yi garkuwa da Nabeeha sun mika gawarta, kuma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, danginta sun yi gaggawar binne ta a ranar Asabar.