Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Remi Tinubu Ta Gana Da Daliban Jami’ar Katsina Da Aka Ceto Daga Hannun ‘Yan Bindiga


Remi Tinubu Ta Gana Da Daliba’an Da Aka Ceto Daga Hanun ‘Yan Bindiga Daga Jami’ar Katsina
Remi Tinubu Ta Gana Da Daliba’an Da Aka Ceto Daga Hanun ‘Yan Bindiga Daga Jami’ar Katsina

Uwargidan shugaban kasar Najeriya Oluremi Tinubu ta tarbi hudu daga cikin dalibai biyar na jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina, da aka ceto kwanan nan daga hannun masu garkuwa da mutane.

Mai dakin shugaban ta tarbi daliban ne a gidan gwamnati a yammacin ranar Lahadi.

A wani yunkuri na karfafa daliban, Mrs. Tinubu ta jaddada muhimmancin ilimi a matsayin makami mai karfi wajen wayar da kai da yaki da illahirin ayyukan ta’addanci.

Hakazalika, mai dakin shugaban, a karkashin kungiyarta ta “Renewed Hope Initiative,” ta bai wa kowacce daga cikin ‘yan matan da aka ceto kyautar Naira miliyan daya da sabuwar kwamfutar tafi-da-gidanka.

Bugu da kari, Mrs. Tinubu ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da Naira miliyan biyu ga iyayen kowace yarinya da aka ceto, da kuma Naira miliyan daya ga mataimakin shugaban jami’ar.

Remi Tinubu Ta Gana Da Daliba’an Da Aka Ceto Daga Hanun ‘Yan Bindiga Daga Jami’ar Katsina
Remi Tinubu Ta Gana Da Daliba’an Da Aka Ceto Daga Hanun ‘Yan Bindiga Daga Jami’ar Katsina

Babbar hadima ta musamman ga uwargidan shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Busola Kukoyi ce ta bayyana wadannan abubuwan a cikin wata sanarwa mai taken ‘Uwargidan Shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu, ta ce ilimi shi ne babban makamin yaki da ta’addanci’.

A nata jawabin, Uwargidan shugaban kasar ta bayyana farin cikinta da dawowar ‘yan matan cikin koshin lafiya, ta kuma bayyana irin kalubalen da suka sha a tsawon kwanaki 70 da daliban suka yi a hannun ‘yan bindiga.

Bugu da kari, ta bukaci ‘yan matan akan kada su bar abin da ya faru da su ya hana su neman ilimi da kuma burinsu na nasara a rayuwa ta hanyar samun ilimi. Ta kuma jaddada muhimmancin mayar da wannan lamari mai cike da kalubale zuwa labari mai cike da nasara, inda ta yaba da jajircewar da suka nuna a lokacin da suke shan wahala a hannun ‘yan bindigan.

Remi Tinubu Ta Gana Da Daliba’an Da Aka Ceto Daga Hanun ‘Yan Bindiga Daga Jami’ar Katsina
Remi Tinubu Ta Gana Da Daliba’an Da Aka Ceto Daga Hanun ‘Yan Bindiga Daga Jami’ar Katsina

Birgediya Janar Olutayo Adesuyi, wanda ya wakilci mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ya jaddada muhimmancin ganawar da uwargidan shugaban kasa ta yi da ‘yan matan da aka ceto, inda ya bayyana irin hadin kan da take bayarwa wajen goyon baya ga shirye shiryen alheri na gwamnatin tarayya wajen kyautata tsaro da ceto rayukan al’umma.

Dakta Aminu Ado, shine mataimakin shugaban jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma a jihar Katsina, kuma ya shaidawa Muryar Amurka yadda suka yi farin ciki da kwato daliban daga hannun ‘yan bindiga.

“Da farko muna godewa Allah kuma a madadin shugaban jami’ar mu muna godewa uwargidan shugaban kasa bisa kulawa da ta nuna, da sauran jami’an gwamnati da suka taimaka, muna godiya kwarai. Allah ya saka masu da alheri, kuma alhamdulillahi zamu ci gaba da daukar matakai daidai gwargwado da addu’o’i don gujewa sake aukuwar irin wannan al’amari,” a cewar Dakta Ado.

Shi ma daya daga cikin iyayen daliban da aka sace, Muhammad Sabah Ibrahim, ya shaida cewa ‘yarsa Rukayyat na daya daga cikin yaran da ‘yan bindigan suka sako a farko farkon lamarin, Sabah yana cewa, “da munyi zaton zasu saki sauran daliban lokaci guda bayan sun saki ‘yata, amma sai daga baya aka saki sauran.”

Bayan haka, Malam Sabah ya shaida yadda suka yi ta fama da ‘yan bindigan inda suka bukaci su bada kudi kimanin miliyan biyar biyar kan kowacce daga cikin ‘yan matan biyar kafin a sake su.

“Mun yi ta rokon su, daga baya suka rage kudin zuwa miliyan dai-daya akan kowacce daga cikin su,” inji Malam Muhammad Sabah.

Iyayen 'yan matan sun hada kudi kimanin naira miliyan hudu da rabi, amma duk da haka 'yan bindigar suka ce kudin sun yi kadan basu saki yaran ba. Daga karshe ‘yan bindigan sun karbi kimanin kudi miliyan Ashirin da dubu dari hudu, sannan suka sake su, inji Malam Sabah.

Ita ma Rukayya Muhammad daya daga cikin daliban da aka sace, ta bayyana yadda aka sacesu da misalin karfe biyu, ta ce ‘yan bindiga 9 ne suka shigo cikin gidan kwana daliban suka sace su.

“Bayan mun yi kimanin kwanaki goma sha biyu a Katsina, sun sa mun yi tafiyar kimanin kwana biyu akan babur kafin muka kai Zamfara, sun yi mana barazanar aurar damu, sun bugemo sosai, amma Allah ya karemu ba su yi fasikanci da mu ba, mun kai kimanin watanni biyu kafin su sake mu,” inji Rukayya.

Ita ma Fatima Abdullahi Bello na daya daga cikin daliban da aka sace, ta bayyana cewa al’amarin daya faru tamkar mafarki ne, kuma baza su so hakan ya faru da wani ba.

“Bama wanka, abincin da suke bamu dusa ne da kuka, babu mai ba manja, kuma da kanmu muke tukawa, in mun diba kuma su yi mana duka, abincin da mutum daya zai ci shi ake bai wa mutane biyar, suna jin jirgi na zuwa sai su dauremu, wai ko da an yi harbi daga cikin jirgin ya samemu ya kashe mu,” inji Fatima.

Dalibar ta shaida farin cikinsu da irin taimakon da uwargidan shugaban kasa tayi musu, kuma sun yi alwashin komawa makaranta har sai sun kammala karatun su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG