Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren 'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 160 A Tsakiyar Najeriya - AFP


Wasu dake gujewa tashin hankali a tsakiyar Najeriya.
Wasu dake gujewa tashin hankali a tsakiyar Najeriya.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 160 a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, a wasu jerin hare-hare kan kauyuka, a cewar jami’an yankin a ranar Litinin.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, adadin wadanda suka mutu ya karu kan wanda rundunar soji ta bayyana a yammacin ranar Lahadi, inda aka ce mutum 16 ne kadai suka mutu a yankin da ya kwashe tsawon shekaru da dama yana fama da rikice-rikicen addini da kabilanci.

Monday Kassah, Shugaban karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato, ya fadawa AFP cewa, “kimanin mutum 113 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hare-haren da aka soma kai wa tun daga ranar Asabar har ya zuwa safiyar Litinin.

Kassah ya ce rukunin ‘yan bindigar sun kaddamar da tsararrun hare-hare ne kan al’ummomi akalla 20, ya kara da cewa sun kuma sami mutum sama da 300 da suka ji raunuka, da aka garzaya da su a asibitocin Bokkos da Barikin Ladi.

Alkaluman kungiyar agaji ta Red Cross sun bayyana cewa an kashe mutum 104 a kauyuka 18 da ke yankin Bokkos yayin da kuma aka ba da rahoton kashe akalla mutane 50 a wasu kauyukan yankin Barkin Ladi, a cewar Dikson Chollol, wani dan majalisar dokokin jihar.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International, ta soki gwamnati bayan hare-haren, tana mai cewa "hukumomin Najeriya sun kasa kawo karshen munanan hare-hare da ake kai wa a kauyukan jihar Filato," a wani sako da ta wallafa a shafin X, wanda a da ake kira Twitter.

Arewa maso Yamma da tsakiyar Najeriya sun dade suna fama da ta’addanci daga ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a kauyuka domin yin fashi da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma, wanda ke kara ta'azzara saboda saurin karuwar jama'a da matsi na sauyin yanayi, shi ma ya ta'azzara tashe-tashen hankula tsakanin al'umma da haifar da tashin hankali.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne da aka zaba a watan Fabrairu, ya yi alkawarin samar da karin zuba jari ga kasar wacce ita ta fi karfin tattalin arziki da al’umma a nahiyar Afirka, a wani yunkuri na tunkarar kalubalen tsaro da ta ke fama da shi.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ne ya hada wannan rahoto.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG