Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Taraban, SP Usman Abdullahi Jada, ne ya tabbatar da faruwan lamarin wa Muryar Amurka.
Mutane sama da dubu daya kuwa suna gudun hijira sakamakon daidaita kauyukansu akalla talatin da biyar da 'yan bindigar sukayi a yankin na Yorro.
Jami’i na musaman mai kula da 'yan gudun hijira na karamar hukumar Yarron, Yarima Usman Abubakar, ya ce a yan zu haka yana da kididdigar 'yan gudun hijira akalla dubu daya wanda suka tantance kuma akwai wasu ma da suke zaune a gidaje cikin anguwani a Jalingo, fadar mulkin jihar Taraba.
A bangaren Jauron da aka kashe kuwa mun tattauna da Jamila Ahmed, wadda mai anguwar kawunta ne, in da ta ce kawunta dai ya shigo gida kanan yan bindigan su ka zo su ka daukeshi su ka tafi da shi.
Ta ce an yi ta maganar kudi amma kafin a kai ma 'yan bindigan kudin sai suka kashe shi kuma haka dai ya jefa su cikin tashin hankali don akwai wasu mutane da dama a hanun 'yan bindigan har yanzu.
A hirar da Muryar Amurka ta yi da Amos Mazan, wanda ya bindigan su ka sace mi shi bappa kuma su kayi garkuwa da ‘yarsa mai shekara goma sha takwas, ya ce ‘yan bindigan sun kona gidaje da dama a anguwansu.
Ya kara da cewa sai da sayar da amfanin gona kafin ya karbo ‘yarsa da ga hannun ‘yan bindigan.
Mastalar rashin tsaro dai a Najeriya, sai kara ta’azzara ya keyi musaman a shiyar arewa maso tsakiyar kasar dama arewa maso gabas .
Ga cikakken rahoton da Lado Salisu ya hada mana:
Dandalin Mu Tattauna