UNGA: Jawabin Shugaban Ghana Nana Akufo Addo A Taron  Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo (AP)

Shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya koka a kan yadda ake gudanar da harkoki, inda ya nanata cewa tun karshen yakin duniya na biyu a shekarar 1945, babu jin dadi, ga damuwa da kuma rashin kwarin gwiwa a kan tsarin shugabanci.

Ya ce wannan hali da muka samu kai a ciki bai tsaya a wani yanki guda daya ba.

Shugaba Akufo Addo ya tabo batun da galibin kasashen Afirka suke magana akai na sake fasalin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta yadda wasu kasashen Afrika za su samu wakilci na dindindin.

A cewar shugaban na Ghana, "mun shaida sau da yawa, manyan kasashen Majalisar da suke kira ga bin dimokaradiya da yin adalci amma suna yin akasin haka a wannan majalisa, sun maida hankali kan son zuciyarsu amma ba batun bil Adama ba.

Shugaban ya kuma yi magana a kan rashin tsaro da yankin Sahel da Yammacin Afirk ke fuskanta.

A ranar Alhamis ake sa ran wakilin hambararriyar gwamnatin Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, zai gabatar da jawabi a zauren majalisar.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

UNGA: Jawabin Shugaban Ghana Nana Akufo Addo A Taron  Majalisar Dinkin Duniya