Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNGA: Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo-Addo Da Tawagarsa Sun Isa Taron MDD Na 78


Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya jagoranci tawagar Ghana zuwa babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ke gudana a hedkwatar Majalisar dake birnin New York na kasar Amurka.

An fara gudanar da muhawara a taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) karo na 78 a yau Talata mai taken: Sake Gina Amana Da Habbaka Hadin Kai Na Duniya; Kara daukar matakai kan ajandar 2030 da muradun ci gaba mai dorewa, samar da zaman lafiya, wadata, da ci gaba ga kowa.

Shugaba Akufo-Addo zai gabatar da jawabi ga Majalisar ranar Laraba 20 ga Satumba 2023. Ana sa ran zai yi amfani da wannan damar wajen nuna matakan da gwamnatinsa ke dauka don aiwatar da dukkan muradun ci gaba mai dorewa guda 17 na Majalisar Dinkin Duniya, da yunkurin da kasar ke yi na farfado da tattalin arzikinta da ya tabarbare sakamakon annobar COVID-19, da kuma yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

Manazarci kan harkokin siyasa da al’amuran yau da kullum Yunus Swalahudeen Wakpenjo, na fatan Shugaba Akufo-Addo zai bayyana matsalolin da al’ummar Ghana ke fuskanta a gaban Majalisar ko kasar ta samu tallafin kudi ko shawara.

“Muna fatan ya fadi gaskiya game da yanayin da kasar Ghana ke ciki, ta bangaren tsaro, tattalin arziki da kokawar da ‘yan kasa ke yi. Akwai bukatar Shugaba Akufo-Addo ya bayyana dukkan matsalolin ga majalisar ko kasar za ta samu tallafi.”

Batun dumamar yanayi na daga cikin manyan batutuwa da za a tattuna a taron, musamman yanzu da duniya ke matsawa daga 2.6 zuwa 2.8 ma’aunin Centigrade na zafin rana a ƙarshen karni na 21, kuma manufar Majalisar Dinkin Duniya ce a nemo hanyoyin da shugabannin duniya za su yi aiki don iyakance dumamar yanayi zuwa 1.5 a ma’aunin centigrade. Tare kuma da manufar siyasa, Majalisar Dinkin Duniya na da yakinin cewa ana iya cimma burin, amma akwai bukatar aiki da yawa.

Mataimakin Daraktan bincike a cibiyar sauyin yanayi da samar da Abinci, Mohammed Jafaru Dankwabia, ya ce zai so Shugaba Akufo-Addo ya gabatar da matsalolin kwararowar ‘yan gudun hijira daga makwabtan kasashe da ake tashin hankali da ke da alaka da dumamar yanayi.

Jafar ya kara da cewa, tilas ne Shugaba Akufo-Addo ya yi wa majalisar bayanin matsalolin cikin gida, musamman ta bangaren fari da ambaliyar ruwa da suka sa manoma rasa hanyar samun abincinsu.

Sannan batun hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba (da aka fi sani da Galamsey a Ghana), wanda ke taimakawa wajen sauyin yanayi, matsala ce da ya kamata Shugaban ya bayyana inda aka kai wajen yakar wannan lamari.

Shugaba Akufo-Addo ya samu rakiyar ministar harkokin waje, Shirley Ayorkor Botchwey da jami'an fadar shugaban kasa da na ma'aikatar harkokin wajen kasar. Ana sa ran zai koma gida a ranar Laraba 27 ga watan Satumba, 2023, kuma mataimakin shugaban kasa, Alhaji Dokta Mahamudu Bawumia ne zai yi aiki a madadinsa, kamar yadda doka ta 60 (8) ta kundin tsarin mulkin kasar ta tanada.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:

Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo-Addo Da Tawagarsa Sun Tafi Taron MDD Na 78.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG