Shugabannin Najeriya da Afirka ta Kudu sun gana ranar Litinin gabanin taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York da zummar karfafa hadin kai tsakanin kasashen musamman ma a bangaren harkar ma’adinai da na sadarwa. Kwararru sun ce samun karin hadin kai tsakanin manyan kasashen Afirkan biyu mafiya girman tattalin arziki a tafarkin yarjejeniyar kasuwanci na bai daya a nahiyar zai bunkasa habbaka ci gaba a fadin nahihiyar.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ganawar shugaban da takwaran aikinsa Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ita ce ganawa ta farko da ake sa ran shugaban zai yi da takwarorinsa aikinsa daga fadin duniya cikin makon nan a wurin taron kolin MDD na 78.
Manufar it ace jawo hankalin masu zuba jari da za su karfafa tattalin arzikin Najeriya.
A ranar Litinin, Tinubu da Ramaphosa sun tattauna yiwuwar hadaka a fannin hakar ma'adinai da sadarwa - takamaimai, batun sassauta dokokin yin kasuwanci da kasar da ke yi wa masu zuba jari kasa a gwiwa.
Tinubu ya ce inganta kawancen kasuwanci zai samar da ayyukan yi kana, kasashen biyu za su amfana.
A lokacin gangamin yakin zabe cikin shekarar nan, Tinubu ya yi alkawarin bunkasa tattalin arzikin Najeriya idan ya yi nasara.
Tun bayan kama aiki a watan Mayu, shugaban ya dau mafi girman matakan seta al’amuran tattalin arziki da aka taba yi a kasar cikin shekaru goman da suka gabata cikinsu har da janye tallafin man fetur din da yayi wa kasar katutu.
Cikin makon nan, ana sa ran cewaTinubu zai gana da shugaban Amurka Joe Biden da kuma shugabannin kamfanin Microsoft, Meta da Exxon Mobil.
Wani mai sharhi kan lamuran siyasa mai suna Rotimi Olawale, ya ce ana kyautata zaton cewa shugaban zai samu irin wannan ganawar da zummar bude kofar shigowar kudaden jari daga masu zuba jari na kasashen waje.
Dandalin Mu Tattauna