WASHINGTON, D. .C. - A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, ta ce shugabannin kasashen biyu na nahiyar Afirka sun gana gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka fara a wannan makon.
"Za mu iya yin hadin gwiwa ta yadda za ta amfani kasashenmu," in ji Tinubu, ya kara da cewa kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa a fannin hakar ma'adinai da sadarwa don taimakawa masana'antunsu "samar da ayyukan yi."
Shugaba Ramaphosa ya yaba da sauye-sauyen tattalin arziki da Tinubu ya yi a Najeriya ya kuma yi alkawarin cewa Afirka ta Kudu za ta kara fadada hadin gwiwa da Najeriya.
"Kasashenmu biyu masu karfin tattalin arziki ne a nahiyarmu, kuma yana da muhimmanci mu zurfafa alakar tattalin arziki, musamman dangane da yarjejeniyar cinikayya cikin walwala ta nahiyar Afirka," in ji Ramaphosa.
"Za mu so mu ga Najeriya da Afirka ta Kudu suna aiki kafada-da-kafada a kan batutuwa da dama, saboda a duk lokacin da muka hada hannu, za mu yi tasiri a duniya ta hanyar hadin gwiwa," in ji shi.
Tinubu ya kuma bukaci Afirka ta Kudu ta hada hannu da Najeriya wajen yin kiran neman sauye-sauye a cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen duniya domin taimakawa Afirka wajen yakar talauci da tabarbarewar tattalin arziki.
"Ya zama wajibi mu hada hannu mu kuma amince cewa cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa na bukatar garambawul domin yanzu Afirka ba wuri ne na kalar harkokin tattalin arziki ba, amma wuri ne da ke da masu hazaka, wanda ke a shirye don masu zuba jari da hadin gwiwa," in ji Tinubu.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna