Ukraine Ta Nemi Kasashen Duniya Su Kai Mata Dauki

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy

A ranar Litinin Shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ya tura dakaru dubu 150 kan iyakar Ukraine, ya rattaba hannun kan wata doka wacce ta ayyana yankunan Donetsk da Luhansk da ke gabashin Ukraine a matsayin masu cin gashin kansu.

Ministan harkokin wajen Ukraine, ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan gaggawa da matsaya ta bai-daya, don kare kasarsu daga fadawa karkashin mamayar dakarun Rasha.

Yayin wani taron Majalisar Dinkin Duniya, Dmytro Kuleba ya ce, burin Rasha ba shi ne ta tsaya akan Ukraine ba, yana mai cewa tsunduma kasar ta Ukraine cikin yaki, zai janyo hatsaniya a duniya.

Ministan ya kuma yi gargadin cewa Rasha ta nuna alamun cewa a shirye take ta fadada wannan mamaya, lamarin da ya ce zai jefa rayukan dakarun Ukraine da na fararen hula da suka hada da yara da mata cikin mummunan hadari.

A ranar Litinin Shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ya tura dakaru dubu 150 kan iyakar Ukraine, ya rattaba hannun kan wata doka wacce ta ayyana yankunan Donetsk da Luhansk da ke gabashin Ukraine a matsayin masu cin gashin kansu.

Ya kuma tura dakarunsa zuwa wadannan yankunan inda ya yi ikirarin cewa sun shiga ne don kare rayukan fararen hula.