Hukumomin Ukraine sun ce akalla kamfanonin jiragen sama 10 ne suka dena zirga-zirga a kasar yayin da Amurka ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar dakarun Rasha da suka taru a kan iyakar kasar su kai hari.
Sai dai gwamnatin ta Ukraine ta ce sararin samaniyarta ba ya tattare da wani hadari.
A ranar Litinin kamfanin Lufthansa na kasar Jamus ya dakatar da zirgar-zirgar jiragensa zuwa kasar.
Matakin na Lufthansa na zuwa ne bayan da kamfanin KLM shi ma ya janye ayyukansa a kasar ta Ukraine wacce ke gabashin nahiyar turai.
Tuni dai kamfanin jirage na Scandinavian SAS shi ma ya dakatar da safarar da yake yi ta mako-mako yayin da shi ma kamfanin Air France ya yanke shawarar soke jigilar da zai yi a ranar Talatar a tsakanin biranen Paris da Kyiv, babban birnin kasar ta Ukraine.
Sai dai hukumomin kasar sun nuna rashin jin dadinsu da wadannan matakai da kamfanonin jiragen ke dauka.
“Soke zirga-zirgar da kamfanonin jiragen kasashen waje ke yi na faruwa ne saboda bayanai da ke kara ruruta lamarin, ba wai don akwai hadari tattare da zirga-zirgar jirage a sararin samaniyar kasar ba.” In ji Ministan manyan ayyuka Oleksander Kubrakov.
Ya kara da cewa, “hukumomin kasar na shirin maye gurbin jiragen da suka soke ayyukansu.”
Wannan labari ne daga kamfanin dillancin labarai na Reuters da Mahmud Lalo ya fassara