Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Ukraine


Abubuwa masu ban mamaki da aka samu a cikin shekarun da suka gabata a cikin Ukraine suna cikin haɗari. Muhimman damammaki na saka hannayen jari ds kutsa kai cikin kasuwannin turai na fuskantar barazana 

Mataki mai mahimmanci don ƙarfafa dimokiradiyya a cikin Ukraine da sauran wurare shine kawar da cin hanci da rashawa. Muggan kasashe irinsu Rasha da China, suna kawance da masu karfin iko don karkatar da doka, don juya tsarin dimokiradiyya daga ciki," in ji Samantha Power, jami’a a hukumar raya kasashe ta USAID, a cikin wani jawabi da ta gabatar kwanan nan ga taron raya tsarin Dimokradiyya da yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaba Biden kwanan nan ya ba da wata sanarwa ta shugaban kasa wanda ke nuna cin hanci da rashawa a matsayin babban abin da za a mayar da hankali akai don tabbatar da tsaron kasa. Takardar yarjejeniyar ta fahimci cewa cin hanci da rashawa na gurgunta al'ummomi, suna yin sata daga aljihun 'yan kasar da ke biyan haraji, yana karya amincewar da jama'a ke yi wa cibiyoyin gwamnati, da kuma rage saka hannun jari na shekaru da dama na duniya don inganta rayuwa.

"Wannan shine dalilin da ya sa yaki da cin hanci da rashawa shine babban burin aikin USAID a Ukraine," in ji Power. Shirye-shiryen yanzu suna aiki don yin amfani da lambobin jama'a, inganta tsarin mulki, sanya albarkatun gwamnati a hannun jami'ai na gari wadanda za su sami kyakkyawar ma'anar yadda za a gudanar da su cikin adalci ko tallafawa kungiyoyin farar hula da masu kawo sauyi a kafofin watsa labarai-kungiyoyi kamar na Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa.

Daga yanzu, USAID za ta tashi tsaye don yaki da cin hanci da rashawa don karfafawa da hade ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a duk fadin hukumar, ta hanyar amfani da ilimin manyan masana na ciki da na waje don magance cin hanci da rashawa a Ukraine da ma wasu kasashen.

Kungiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa za ta sake nazarin shirye-shiryen USAID na yanzu don gano yadda za a iya amfani da taimakon ƙasashen waje don iyakance da hana cin hanci. Kungiyar za ta kuma jagoranci haɗakar hanyoyin yaƙi da cin hanci da rashawa a duk faɗin shirye-shiryen sashen na USAID da kafa wata hanyar mayar da martani cikin hanzari don kame manyan hanyoyi dama na sauye-sauyen demokraɗiyya da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Sabon kasafin kudin na Shugaba Biden ya bayar da dala miliyan 50 don wannan sabon kokarin nan na gaggawa. Amurka na fatan fadada wadannan alkawurra tare da karfafa gwiwar sauran kasashe su yi nasu a taron koli na demokradiyya mai zuwa karkashin jagorancin Shugaba Biden, wanda zai nemi alkawurran da ke ciyar da dimokiradiyya gaba, yaki da cin hanci da rashawa, da kare hakkin dan adam.

“Ina son kowa da kowa a cikin wannan dandalin ya sani,” in ji Mai Gudanarwa Power, “Kasar Amurka na tare da ku, yayin da kuke kokarin gina duniya mai gaskiya, adalci, da demokradiyya.

XS
SM
MD
LG