Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Ya Take Dokar Kasa Da Kasa - Biden


APTOPIX Biden
APTOPIX Biden

A ranar Litinin Putin ya Ayyana wasu yankunan Ukraine a zaman masu cin gashin kansu, wadanda ba sa karkashin kasar.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yanke gwamnatin Rasha daga harkokin kudi na kasa da kasa a ranar Talata, sannan ya kakaba wa manyan bankunanta biyu takunkumi, inda ya ayyana shigar sojojinta cikin gabashin Ukraine a matsayin “sabawa dokar kasa da kasa.”

A wani takaitaccen jawabi a Fadar White House zuwa ga Amurkawa, Biden ya ce, bada umurnin da shugaban Rasha Vladimir Putin yayi a ranar Litinin na tura dakarunsa a fadin gabashin iyakar Ukraine zuwa lardunan Luhansk da Donestsk shi ne “farkon mamayar Ukraine da Rasha ke kokarin yi.”

A ranar Litinin Putin ya Ayyana wasu yankunan Ukraine a zaman masu cin gashin kansu, wadanda ba sa karkashin kasar.

Shugaban Amurkan ya ce takunkumin zai yanke gwamnatin Rasha “daga samun kudade daga Yamma,”sannan ya dau alkawarin cewa Rasha “za ta dandana kudarta da wasu tankunkumai masu yawa, idan har sojojinta suka ci gaba da mamaya a cikin Ukraine.

"Idan har Rasha ta ci gaba da mamayar da take yi, mu ma a shirye muke mu kara sabbin takunkumi, shin waye ya ba Putin ikon ya ayyana wasu yankuna a matsayin sabbin kasashe da suka kasance mallakar makwabtansa? Wannan take dokar kasa da kasa ce karara.” Biden ya ce.

A ranar Litinin, yayin jawabi a Kremlin, Putin ya ayyana cewa Ukraine ba ta taba zama kasa mai ‘Yancin kanta ba, sannan kuma mallakin babbar tarrayar Rasha mai tasiri, ba ‘Yar amshin shatan’ Yamma ba ce.

Wannan labari ne na kamfanin dillancin labarai na AP da Mahmud Lalo ya fassara.

XS
SM
MD
LG