Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Saka wa Rasha Takunkumi Kan Ukraine


Shugaba Biden yana rattaba hannu kan dokar saka takunkumi ga Rasha bayan da Putin da ya ayyana wasu yankunan Ukarine biyu a matsayin masu 'yanci (Foto: Twitter/@POTUS)
Shugaba Biden yana rattaba hannu kan dokar saka takunkumi ga Rasha bayan da Putin da ya ayyana wasu yankunan Ukarine biyu a matsayin masu 'yanci (Foto: Twitter/@POTUS)

“Da ma mun yi tsammanin Rasha za ta dauki irin wannan mataki, kuma a shirye muke mu mayar da martini.” Sakatariyar watsa labarai a Fadar White House Jen Psaki ta ce a ranar Litinin.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta saka wa Rasha takunkumi kan mamaye yankunan Donetsk da Luhansk da ta yi a gabashin Ukraine.

Sanarwar daukan wannan mataki na zuwa ne sa’o’i bayan da Shugaba Vladimir Putin ya ayyana wadannan yankunan a matsayin masu cin gashin kansu.

“Da ma mun yi tsammanin Rasha za ta dauki irin wannan mataki, kuma a shirye muke mu mayar da martini.” Sakatariyar watsa labarai a Fadar White House Jen Psaki ta ce a ranar Litinin.

Ta kara da cewa Shugaba Joe Biden zai yi doka ta kashin kansa da za ta haramtawa Amurkawa yin sabbin huldodin kasuwanci a wadannan yankuna.

Wannan mataki da Putin ya dauka ya kara jaddada fargabar da kasashen yammacin duniya ke nunawa, na yunkurin mamaya da Rasha ke shirin yi wa Ukraine, lamarin da ya sa wani babban jami’in gwamnati ya fadawa manema labarai cewa wannan barazana ce ta hakika.

“Cikin sa’ar da ta shude, mun ga yadda Rasha ta ba dakarunta umarnin shiga Donetsk da Luhansk, kan ikirarin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya.” In ji jami’in.

Ya kara da cewa, Fadar ta White za ta ayyana karin wasu takunkumi a ranar Talata kan wannan lamari da bayyana a matsayin take dokar kasa da kasa da keta diyaucin Ukraine.

Fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya ya fadawa shugabannin Faransa da Jamus a ranar Litinin kan wannan shirin ya kuma rattaba hannu kan wasu takardu da zimmar ayyana wadannan yankuna a matsayin ba mallakar Ukraine ba ne.

Shi dai Putin ya tara dakarunsa dubu 150 a Belarus, arewa da Ukraine da kuma yankunan gabashi da kudancin iyakokin Ukraine.

Wannan labari ne da Anita Powell da Ken Bredemeier suka rubuta wanda Mahmud Lalo ya fassara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG