Turkiyya Zata Girka Wasu Matakan Kariyar Rokokin ISIS

Ministan tsaro na kasar Turkiyya yace saura abu kadan kasar tashi ta kamalla hadawa da girka wasu matakan kariya da zasu rinka yi mata rigakafin rokokin da ISIS zata iya cillo wa biranenta da alkaryu.

Ministan tsaro, Fikri Isik yace wannan sabon shirin kariyar wanda tun kamar wattani 18 da suka gabata aka fara kokarin girka shi, a cikin wannan makon ne za’a soma gwada shi.

A cikin shekara guda da ta gabata dai, Turkiyya tayi fama da shan luguden rokoki da mayakan ISIS ke harbo mata daga cikin Syria.

Daya daga cikin garuruwan Turkiyya da ya sha jin jiki daga wadanan rokokin shine birnin Kilis wanda ta haka ne aka kashe mutane 21 a cikinsa, kuma an nakkasa unguwanni da dama, har abin ya tilastawa mazauna garin su gudu, su bar shi.