WASHINGTON, DC —
A jiya ne Hukumar Zabe ta kasar ta yi wannan jan kunnen cewa za’a ci gaba da bata lokaci idan ba sauri aka yi aka warware maganar yankunan Hiran da Middle Shabelle ba, yankunan biyu da ake jira a tabattarda sahihancinsu kafin a shirya zabukkan.
Yanzu haka gardama ta kaure ma a tsakanin shugaban Somalia din da Frayim-ministansa akan ma wurin da za’a zaunar da sabuwar majalisar lardi ta yankuna, inda shugaba ke cewa a jiye ta a Mogadishu, babban birnin kasar, PM kuma na son a barta a cikin yankin kansa.
Tsiyar abin shine cewa da shugaban kasar da PM din dukkansu ‘yan takaran shugabancin kasar ne kuma suna cikin wannan cibiyar da ake jiran ta yanke shawara akan makomar wadanan yankunan biyu da ake jiran kamalla zancena kansu.