Shugaban kasar Colombia, Juan (Huwan) Manuel Santos yace ba zai bada kai, bori ya hauba duk da kayen da ya sha a kuri’ar raba gardaman da aka jefa jiya mai alaka da yarjejeniyar sulhu da mayakan ‘yantawaye na kungiyar FARC.
Da kuri’u kalilan al’ummar kasar suka kada yunkurin, inda kashi 50 da digo 2 cikin 100 suka ki goyon bayan yarjejeniyar, yayinda kashi 49 da digo 7 cikin 100 suka goyi bayan yarjejeniyar. Duk da cewa shugaba Santos ya shiga tashar telbijin ya amsa cewa ya sha kaye a wannan kuri’ar, duk da haka yace ba zai yanke kauna da ci gaba da yin sulhu da ‘yantawayen ba..
Ya kuma umurci mukarabbansa da cewa su koma birnin Havana na Cuba, inda a acan ne aka share shekaru hudu ana kokarin cimma yarjejeniyar sulhun.
Shima madugun kungiyar mayakan FARC, Rodrigo Londono, yace shima ba zai daina kokarin ganin an cimma sulhu tsakaninsu da gwamanti ba.
Sassan biyu dai suna koakrin sulhunta tarzomar nan ce da ta samo asali tun cikin shekarun 1960, wacce kuma ta raba miliyoyin mutane da matsugunansu kuma tayi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu dari biyu da hamsin.