Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Clinton da Trump Na Musayar Yawu Akan Takardun Harajin Trump


Trump na jam'iyyar Republican da Clinton ta jam'iyyar Democrat
Trump na jam'iyyar Republican da Clinton ta jam'iyyar Democrat

Kungiyar kamfe ta ‘Yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton da ta Donald Trump sunyi musayar yawu, sakamakon buga wani bangare na takardun harajin da ake kyautata zaton na dan takarar jam’iyyar Republican ne na shekarar 1995 da jaridar New York Times buga.

An turawa jaridar ta New York Times din ne takardun a asirce, wadanda suka nuna Trump yayi asarar Miliyan $916 a shekarar 1995 wanda hakan ya baiwa attajirin damar kin biyan haraji na shekaru 18 da suka gabata domin ya mayar da adadin abinda yayi asara.

Wannan ala’mari dai ya fito ne bayan da ‘Yar takarar Democrat Clinton ta cigaba da kalubalantar Trump dangane da yadda yake tafiyar da harkokin kasuwancinsa a ranar Asabar da ta gabata sakamakon kin bayyana takardun sa na haraji da biya.

Kungiyar Kamfe ta Clinton ta bayyana a rubuce cewa Trump yayi asarar kimanin Dala biliyan guda, shiyasa yasa bai iya biyan haraji ba alhali kuwa sauran iyalai da ma’aikata na biyan nasu harajin.

Kungiyar Kamfe ta Mr. Trump ta bayyana cewa takardun harajin da aka bayyana na wajen shekaru ashirin ba a bayyana su ta hanyar da ta dace ba. Wannan yana nuna cewa New York Times da shauran gidajen jaridu nayiwa Hillary Clinton Kamfe ne kawai.

XS
SM
MD
LG