Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Taliban Sun Kutsa cikin Kunduz dake Arewacin Afghanistan


'Yansandan Afghanistan Na Sintiri cikin Birnin Kunduz, birnin da 'yan taliban suka kaiwa farmaki daga wurare daban daban
'Yansandan Afghanistan Na Sintiri cikin Birnin Kunduz, birnin da 'yan taliban suka kaiwa farmaki daga wurare daban daban

Jami’ai a Arewacin Afghanistan sun bayyana cewa Yan Taliban sun kai farmaki a Kunduz, kuma tsageran sun samu shiga cikin wannan birni.

Hukumomi sun ce wannan farmaki na yau Litinin da safe, an kai shi daga kusurwoyi da dama na birnin, kuma dakarun tsaro suna ci gaba da kokarin fatattakar tsageran.

Kakakin 'yansanda, Mahfouzullah Akbari, yace Yan Taliban din sun shiga cikin gidajen fararen hula don haka dole ne suyi taka tsantsan wajen aiwatar da aikinsu.

Mai Magana da yawun Taliban yace dakarunsu sun kama wuraren shiga cikin gari da dama kuma sun kashe sojoji da dama. Amma kalamin na mai Magana da yawun Taliban din ba’a tabbatar dashi ba.

Wannan hari na Taliban yazo daidai lokacin da Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani yake tattaunawa da wasu masu bada gudummuwa a Brussel domin neman kudin da za’a gyara kasar da yaki ya daidaita.

A watan Satumbar shekarar 2015 yan Taliban suka kama garin na Kunduz na tsawon kwanaki kafin su janye.

Dakarun kasar Afghanistan da Sojojin Amurka da na NATO ke taimakawa. Sun maida kai ne wajen hada karfi da karfe a wannan shekarar su kare biranen dake lardunan Arewacin kasar ciki har da Kunduz da Helmand dake kudancin kasar.

Amma hare haren da masu kishin musuluncin ke kaiwa sun kara tsananta musamman a gabashi da kuma kudu maso gabashi da kuma tsakiyar Afghanistan, hakan ya matsawa jami’an tsaron na Afghanistan da tuni sun barbazu a fadin kasar.

XS
SM
MD
LG