Tsarin Taron Kasa na Yanzu Ya Banbanta da na Da

Shugaban kasa da shugaban taron kasa

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa da na yau da kullum yace tsarin taron kasa na yanzu ya banbanta da na da can inda al'umma ke zaban wakilai ba gwamnati kamar yadda aka yi a wannan karon.
A firar da abokiyar aiki tayi da Ahmed Abubakar Dakta wani mai sharhi kan harkokin siyasa da na yau da kullum ya bayyana irin banbancin dake akwai tsakanin tsarin taron yanzu da na da can da a ka yi a kasar.

Tun daga lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kai an yi taron kasa ba sau daya ba ba sau biyu ba kan yadda za'a daidaita abubuwa a kasar domin a cigaba. Tun zamani su Sardauna a ke yin kokarin a kawo shawarwari domin a samu daidaitawa.

Kowane taron idan za'a yi akwai wasu tsare-tsare da a ke yi ba yadda a ka gani a wannan lokacin ba. A wadancan lokutan a kan zabi mutane ne, wato al'ummomi ne ke zabar mutanen da zasu wakilcesu. Amma a wannan taron shugaban kasa da gwamnoni su ne suka zabi mutanen da suke so su je taron. A wannan taron mutane ba'a bari sun zabi wadanda zasu wakilcesu ba.

Abu na biyu kafin a yi taro a kan tsara manufofin taron da yadda za'a gudanar da shi. Za'a kuma tsara ka'idodin yadda za'a gudanar da shi. Amma wannan taron saidai mutane suga takarda cewa an zabesu. Kana babu wanda ya fada masu abubuwan da zasu yi. A taron babu wakilci na al'umma daban daban. Misali a ce kabilar Hausa nada wakilcin mutane kaza na Yarbawa nada wakilcin mutane kaza da dai sauransu. Wato a raba wakilan kan yawan mutanen Najeriya. Haka kuma a ce Musulmai nada wakilcin mutane kaza Kirista kuma mutane kaza a'a ba'a yi haka ba. An zabi wakilai ne kawai bisa wasu ra'ayi lamarin da ya sa wasu suka fi wasu yawa.

Ranar taron da a ka fara su kansu wakilan basu san me zasu gabatar ba. Abun da aka yi an dauko tsofofin rahotannin taruruka da tsofofin kundurin tsarin mulkin kasa an basu sati daya su je su karanta. Abun tambaya a nan shi ne yaya za'a yi a ce cikin sati daya kowanensu ya karance manya manyan littafai ya samu fahimtar da zai iya yin muhawara a kansu. Abun da kuma ya daure ma mutum kai shi ne wai ka'idodin taron an rubuta sai sun zauna mako mai zuwa su amince. Saboda haka taro ne da aka shirya ba tare da an shirya ba.

Ga cikakkiyar firar

Your browser doesn’t support HTML5

Tsarin Taron Kasa na Yanzu Ya Banbanta da na Da - 9'27"