Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kasa Bashi da Ikon Kafa Doka


Shugaban taron kasa Justice Idris Kutigi
Shugaban taron kasa Justice Idris Kutigi

Yayin da 'yan Najeriya ke tofa albarkacin bakinsu gameda taron kasa 'yan majalisa sun ce taron bashi da ikon kafa doka

Duk da rarrabuwan kawunan 'yan Najeriya kan taron kasa wasu 'yan majalisun dokokin tarayya sun ce taron bashi da ikon kafa doka sai dai ya bayar da shawara.

Wasu na murna wasu kuma na kushewa da taron kasa da a keyi a Abuja yanzu. Sai dai furucin shugaban kasa ya dauke hankalin mutanen Najeriya da dama. Lokacin da yake bude taron shugaban kasa yace ana iya tabo batun mallakar arzikin yanki da rage karfin ikon gwamnatin tarayya da kirkiro sabbin jihohi da kuma barin kananan hukumomi su ci gashin kansu.

Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi a Najeriya Ibrahim Khalil na cikin masu farin ciki da taron. Yace tsa'arin mulkin kasar bai tanadi hukumar kula da kananan hukumomi ba lamarin da ya sa gwamnoni suka sasu a hammatarsu. Sabili da haka an bar kananan hukumomi kara zube kana gwamnoni na facaka da kudadensu yadda suka ga dama. Haka ma wani wakili daga arewa maso gabas Yerima Muri na ganin taron zai tabbatarwa al'umma bukatunsu.

Kodayake shugaban kasa Jonathan ya kare taron da cewa bai sabawa mulkin kasar ba amma Sanata Kabiru Gaya bai amince da maganarsa ba. Yace taron na bannatar da kudin Najeriya ne domin babu dokar da taron zai iya yi. Duk abun da suka fada shawara ce kuma an dade ana bada shawara. Ita shawarar ba zata yi tasiri ba sai an kaita majalisa a mayarda ita doka kafin ta yi wani aiki. Amma kuma 'yan majalisar wakilai da na dattawa su ne ainihin wakilan Nakeriya. Su ne ya kamata su bada shawara. Amma an dauki mutanen da za'a yi masu komi da biyansu makudan kudi su bayar da shawarar da ba zata yi aiki ba.

Duk abun da zai zama doka sai an kaishi majalisa. Amma kuma nan da wata shida 'yan majalisa sun fara fafitikan neman zabe lamarin da ya sa babu wani lokaci da majalisa ke dashi na duba shawarwarin da taron zai tsayar. Yanzu mutanen kudancin kudu sun hakikance a basu dari bisa dari na kudin man fetur da ake hakowa. Amma kuma wasu a arewa sun ce ai ma kason da ake basu yanzu ma bai cancanta ba. Irin wannan banbancin ka iya kawo takaddama.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG